Kwalejin koyan tukin jirgin sama na Najeriya NCAT dake Zariya za ta siyo sabon jirgi ‘Boeing 737 Simulator’ a shekarar 2018.
Shugaban kwalejin Mohammed Abdulsalam ne ya sanar da haka da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Abuja.
Yace kwalejin za ta siya wannan jirgi ne don Kara bunkasa koyan tukin jirgin sama ga dalibai.
Ya ce kwalejin ta biya kashi 70 bisa 100 na kudin jigin.
Za a siyo jirgin daga Kasar Canada ne.
Discussion about this post