Kungiyar malaman kwalejojin Kimiyya da Fasaha ASUP ta fara yajin aiki

0

Shugaban kungiyar ASUP na kasa Usman Dutse ya ce kungiyar ta yanke shawaran fara yajin aiki ne bayan watsi da su da gwamnatin tarayya ta yi kan alkawarin da ta dauka a zaman su a baya.

Dutse ya ce ” mun amince cewa ma’iakatan Kwadago za ta aiko mana da cikakken bayanai kan abubuwan da muka tattauna a zaman mu na karshe. Amma har rana kamar ta yau shiru kake ji. Babu abin da ta yi akai. Mu kuma mambobin mu suka ga ba za su iya daukar irin wannan wulakancin ba muka yanke hukuncin fara yajin aikin.”

Ya kara da cewa ko daya ke suna da zama da gwamnati ranar 15 ga watan Nuwamba, duk da haka za su fara yajin aikin.

Share.

game da Author