Kungiyar Izala ba ta karbi kudin Makamai ba – Kabiru Gombe

0

Sheikh Kabiru Gombe, na Kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah, ya Karyata rade-radin da ake ta yada wa wai kungiyar ta karbi wani abu daga ‘kudin makamai’.

Sheikh Gombe ya bayyana haka ne a wata ziyara da ya kai ofishin BBC Hausa a garin Landan tare da rakiyar shugaban kungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau,

A hirar da ya yi da BBC Hausa, Sheikh Gombe ya ce tabbas kungiyar Izala ta nemi taimako daga wurare da yawa domin yin wasu ayyukan ta da ya hada da bude gidan talabijin na Manara TV, amma kungiyar ba ta da alaka ta kusa ko ta nesa da maganar karbar kudin makamai.

Ya kara da cewa duk inda suka sami gudunmawa sai da suka tabbatar hanya ce da ta dace.

“Ba mu da alaka ta kusa ko ta nesa da maganar karbar kudin makamai. Wannan abu ne da kungiyar Izala ba ta taba shiga cikin shi ba,”

Share.

game da Author