Yadda kishi ya dauko wani sabon salo yanzu musamman a yankin Arewacin Najeriya, abin ya na tada wa iyaye da musamman mazaje hankali.
Mafi akasari mutum musulmi, kai har wanda ba musulmi ba a yankin arewacin Najeriya ya taso ne ya ga ubansa da mata biyu, uku, ko hudu ko kuma a gaban sa aka karo wata ko kuma uwar sa ce amaryar.
Kwarai ana kishi amma kishin su a wancan zamani na yadda za a karkato hankalin Alhaji ne zuwa ga uwargida ko amarya. Ana kishi ne domin burge maigida da dadada masa rai. Sannan kuma kishin su baya wuce tsakanin su iyaye.
Babu abin da zai sa wata tayi ma dan wata mugunta. ‘Dan na kowa ne’. Haka zaka ji suna fadi.
Suna zama a gida daya ne, a dafa abinci a tukunya daya a taru waje daya a ci abinci.
ZAMANI YA CANZA
A wannan zamanin kuwa abin ya canza salo matuka. Kwanankin baya wata gidan jarida ta ruwaito labarin wata mata da ta zane jikin yar kishiya da sabuwar reza saboda kishi. Haka kuma wata ta kama azzakarin dan yaro karami, dan kishiya ta yanke su. Idan aka ce za a ci gaba da fadin irin wadannan abubuwa zamu kwana muna fadi.
Maza suma basu tsira ba daga irin wannan masifa da ya shigo mana.
Wata mata ta taba kona mijin ta har lahira saboda hira da suka yi yayi mata ba’a cewa zai kara mata. Yana barci da daddare ta dauko jarkar kalanzir ta dul-dula masa tako kyasta ashana, kafin kace wani abu ya kone.
Bayan fama da asiri da tsubbace tsubbace da maza ke sha daga wajen matan su, abin dai ya zama abin tsoro ga maza a wannan zamani da muke ciki domin yanzu idan ka kubuta daga wannan sharri, sais u kashe ko da makami ko kuma a kona ka.
Haka kuma a wannan mako labarin da yake ta zagayawa shi ne na kisan dan tsohon shugaban jam’iyyar PDP Bello Halliru kamar yadda ake ta yadawa a kafafen yada labarai, dana yanar gizo wai matar ta daba masa wuka a zuciyar sa saboda ya tura sakon tes ta wayar sa. Ita kuma tayi zaton hira yake yi da mata ta yanar gizo. Da ta fusata sai ko ta daba masa wuka a zuciyar sa sannan ta dauke shi zuwa asibiti, kafin ayi watawata Allah yayi masa cikawa.
An kama wata mata cikin dare a makabarta ta zo tana birni layu da wasu gulungutayya. Da aka bude sai aka ga wai mijin ta tayi wa a garin Kaduna. Haka dai za kayi ta ji abin ba dadi.
Abin da zai baka tsoro da mamaki, shine kusan duk irin wadannan mata sukan ce suna zuwa Islamiyya kullum, ko kuma sun sami karatun addini a gidajen iyayen su kafin su yi aure. Sannan da yawan su ma a gidan yawa suka fito inda iyayen su maza mata fiye da daya suke da.
Bincike da na yi ya nuna cewa yaran da suke aikata irin wadannan ayyuka duk basu wuce shekaru 35 zuwa kasa, duk da cewa akwai wadanda shekarun su ya fi haka yawa.
Idan ka duba wannan lamari fa lallai akwai sakaci na maza da kuma iyaye. Tun farko ya kamata a nuna wa ‘ya cewa ba lallai bane ta zauna ita kadai a gidan mijin ta idan har itace ta farko sannan a karantar dasu abin da addini ya ce gami da aure da zaman sa.
Marigayi Mal. Mai-Iyali na masallacin Juma’a na Barnawa ya taba, yi wa mutane nasiha cewa sau dayawa wasu matan bana zama bane, idan kai namiji ka gane tana da irin wadannan halaye da baza ka iya jurewa ba sakin ta shine mafi alkhari domin za ta iya samun wanda shi kuma daidai da ita yake.
Addu’a shine mafita, sannan malamai su yawaita fadakar da mata game da zaman aure.