KISHI: Mata ta hau mijin ta da duka a jirgin sama da yasa dole aka ya da Zango don canza musu jirgi

0

Wani abu kamar almara da ya faru a cikin jirgin saman ‘Qatar Airways’ ya bar fasinsojin da sallallami inda har yasa jirgin tayi saukar gaggawa a filin jirgin saman Chennai, dake kasar India.

Wata mata ce da mijin ta suka taso daga Doha zuwa Bali. Lokacin da mijin ya dan yi likimo a jirgin sai ko ta daga hannun sa ta bude wayar sa ta ko gano ma kanta abin da ya tada mata da hankali.

Bai ankara ba gogan naka cikin barci ta dunga cusa masa naushi. Farkawar sa ke da wuya kuwa sai jirgi ya hargitse aka. Rikici ya kaure.

Da matuka jirgin suka ga abin dai ba sauki sai suka nemi sauka a filin jirgin Chennai, kasar India.

Da jirgi ya sauka kuwa sai aka mika su ga jami’an tsaro. Bayan komai ya lafa aka sa su a wani jirgin zuwa Bali. Su ko ‘yan wancan jirgin tuni suka kama gaban su.

Share.

game da Author