Kashi 70 bisa 100 na magungunan da ke yawo a Najeriya ba Jabu ne – NAFDAC

0

Hukumar Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta karyata rahoton jaridu da ake ta yadawa wai kashi 70 bisa 100 na magungunan da ke yawo a kasar nan jabu ne .

Wani babban Jami’i a gidauniyar ‘Project Blue PWc’ Andrew Nevin ya ce kashi 70 bisa 100 na magungunan dake yawo a Najeriya jabu ne.

Ya fadi haka ne a taron da kungiyar masu sarrafa magunguna a Najeriya PSN ta shirya a Umuahia jihar Abia.

Ya bayyana cewa a nahiyar Afrika mutane 100,000 ne suke rasa rayukan su duk shekara dalilin amfani da jabun magani.

Sai dai kuma a martanin da Darekta a hukumar Abubakar Jimoh ya ce wannan lissafi da Nevin ya kawo ba haka bane, babu gaskiya a cikin sa ko kadan.

” Bamu san inda mutumin ya samo bayanan sa ba. Kawai irin maganganun nan ne da ake yi da basu da madafa. Haka kawai ba ma amsa irin wadannan maganganu idan aka yi su, amma cewa da yayi wai shi kwararre ne ya sa muka ga ya dace a mai da masa martani saboda kada mutane su dauka haka ne.

Share.

game da Author