Sojin Kasar Zimbabwe sun karbe ikon gidajen Talabijin da Rediyon kasar, inda suke ta shawagi a manyan titunan babban birnin Kasar, Harare.
Sojin sun sanar cewa shugaban kasar, Robert Mugabe na cikin koshin Lafiya a inda suke tsare da shi.
Mugabe ya kai kusan shekaru sama da 30 yana mulkin kasar Zimbabwe sannan yanzu ya kai ga baya iya yin komai ma sai dai matar sa.
Duk da soyayyar da mutanen sa ke masa abin dai da kamar wuya.
Sojojin sun kama manyan ‘yan siyasar kasar da wasu jami’an ‘yan sanda.
Discussion about this post