Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu, ya bayyana rashin jin dadin sa ganin yadda kabilanci da addinanci suka kara raba kawunan ‘yan Najeriya.
Ekweremadu ya yi wannan bayani ne a wurin taron shekara-shekara wanda aka tattauna batun masu rajin ballewa daga Najeriya, a Abuja.
Mataimakin ya ce abin takaici kuma wannan rarrabuwar kawuna sai karuwa ta ke yi a wannan lokaci. Ya na mai cewa idan aka kalli kasar nan a yanzu, za a iya cewa ba a daidai ta ke tafiya kan siradin da ya kamata ta tafi ba.
“Irin yadda ake antaya wa juna ruwan munanan kalamai da zagin-kare-dangi tsakanin matasan wannan kabila da na waccan, ko mabiyan wannan addini da na wancan a kafafen soshiyal midiya, to hakan na nuna cikin duhu ma mu ke kara dulmiyawa, maimakon a ce kasar nan gaba ta ke kara ci.
“Don haka ni ina ganin lokaci ya yi da za mu fada wa kanmu gaskiya, kuma a zo a zauna kan teburi a tattauna matsalar mu. Ina kuma da yakinin cewa dauko daftarin taron kasa na 2014 shi ne matakin farko da ya kamata a fara dauka.
A karshe ya ce ya yi imanai idan aka zauna aka kafa wani ginshikin sake dunke barakar kasar nan, to Najeriya za ta ginu fiye da yadda kowa ke tunani.