Jihohin Imo, Ogun da Kano sun fi yawan wadanda Buhari ya nada mukamai

0

Ba kamar yadda jaridar Business Day ta ruwaito ba cewa mutane 81 cikin 100 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada ‘yan yankin Arewa, mai ba shugaban kasa shawara kan harkar yada Labarai Femi Adesina ya fito karara ya musanta haka.

Femi ya ce wannan jarida bata hi bincike yadda ya kamata ba. Ya ce akwai da yawa cikin wadanda aka nada da jaridar bata ambato su ba a rahoton ta.

A bayanan da Femi ya yi, jihar Ogun ta fi yawan wadanda Buhari ya nada a gwamnatin sa inda ta ke da mutane har 21. Daga nan sai Kano da Imo da suke da 15 kowannen su.

Jihar Edo da Katsina ce ta hudu da mutane 14 kowannen su.

Babban birnin Tarayya ce a karshe inda ko maigadi ba a nada ba.

Jihohin Ebonyi da Abia na da bibbiyu, Kebbi na da Uku,

Jihohin Zamfara, Sokoto, Oyo, Enugu, Ekiti da Akwa Ibom kuma suna da hurhudu.

Share.

game da Author