Jihar Sokoto ta kaddamar da shirin daukar dalibai

0

Gwamna Aminu Tambuwal ya kaddamar da shirin daukar daliban firamare, wanda ya ce shi ne mafi girma kuma mafi yawa, inda jihar za ta dauki yara miliyan 1.4 a cikin shekara daya mai zuwa.

An kaddamar da shirin daukar daliban ne a kauyen Riji da ke cikin Karamar Hukumar Rabah. An kuma yi amfani da lokacin aka kaddadmar da shirin bai wa yara ‘yan makaranta tallafi, wanda hadin guiwa ne NPEP da kuma ECD.

Kauyen Riji dai can ne mahaifar tsohon Firimiyan Arewa, Ahmadu Bello.

Da ya ke jawabi a lokacin taron, Tambuwal ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da kashe makudan kudade da kuma sadaukar da lokaci mai tsawo wajen inganta fannin ilimi.

“Wannan shirin na daukar dalibai da yawan gaske, abu ne da aka yi wa babban shiri wanda ake bukatar duk masu ruwa da tsaki su shigo ciki, domin su taimaka wajen wayar da kai. Ya kuma kunshi iyaye, shugabannin cikin al’umma da kuma shugabannin addinai. Za su wayar wa jama’a kai dangane da muhimmancin tura yara makaranta.

A ta bakin sa, shirin zai dogara ne kacokan wajen bi gida-gida da lungu-lungu ana wayar wa mutane kai dangane da muhimmmancin ilimi.

Da yake jawabi, kwamishinan ilimin firamare da na sakandare, Jabbi Kilgore, ya ce duk da dai muradin su shi ne daukar dalibai milyan daya da dubu 400, hakan zai iya yiwuwa domin shirin zai hada ne har da shirin maida makarantun Islamiya 4000 inda za a hada su ko a maida su na zamani.

Share.

game da Author