Sakataren ma’aikatar Ilimi na jihar Neja Yahaya Garba ya ce gwamnatin jihar ta gyara ajujuwa 5,065, ta gina sabbi 123 sannan ta gina bandakuna 2,096 a wasu zabbabun makarantu a jihar.
Gwamnati ta kashe Naira biliyan 4.3.
Garba ya ce gwamnati ta zuba sabin kujeru a ofisoshin malamai da wasu makarantu da aka zaba a jihar.
Ga jerin makarantu:
1. Government Girls Modern School Bida
2. Justice Idris Legbo Science College Kutigi
3. Government Science College Baro
4. Maryam Babangida Girls Science College Minna
5. Government Science College Izom
6. Government Secondary School Tegina
7. Mu’azu Commercial College Kotangora
8. Government Girls Science School Kotangora
9. Government Secondary School,Rijau.
Bayan haka Garba ya ce gwamnati ta hada hannu da jami’ar ‘Blaze’ don horar da malaman makarantun da ta gyara kan harkar koyar da kasuwanci.
Ya ce za a fara horar da malaman ne a wannan wata na Nuwamba sannan an samar da Naira miliyan 10 domin hakan.
Daga karshe yace gwamanti ta raba Naira miliyan 170 wa dalibai 7503 ‘yan asalin jihar dake karatu a jami’o’in kasar sannan da Naira miliyan 55 wa dalibai 105 dake karatu a kasashen waje.
Discussion about this post