Jam’iyyar APC tayi babban kamu

0

Daya daga cikin ‘ya’yan tsohon jagoran neman kafa kasar Biafra Odimegu Ojukwu, Emeka Ojukwu jnr ya shiga jam’iyyar APC.

Ojukwu ya fadi haka ne yau a garin Awka a lokacin da shugaban kasa yake kaddamar da dan takaran jam’iyyar APC a zaben gwamnan dake tafe.

” Ina so in sanar muku cewa na fita daga inuwa zuwa haske yanzu. Zan yi duk abin da zanyi don ganin dantakaran mu na jam’iyyar APC ya samu nasara a zaben jihar mai zuwa.

Share.

game da Author