Jam’iyyar APC ta taka rawar gani a Zaben Anambra

0

Jam’iyyar APC ta taka rawar gani a Zaben gwamna da akayi a jihar Anambra.

A sakamakon Zaben da aka sanar na kananan hukumomi 21 dake jihar jam’iyyar itace ta zo na biyu a kananan hukumomi 14.

Jam’iyyar PDP da ake ganin tana da gindin Zama a jihar ce ta uku a yawàn kuri’u.

Masu yin sharhi kan zaben sun ce hakan ya kawo sabon salo a Zaben jihar sannan Kuma nuni ne cewa yankin kudu maso gabas sun fara amsar jam’iyyar a yankin.

Idan ba a manta ba shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya Kai ziyara jihar Anambra domin tallata dan takaran gwamnan jihar Tony Nwoye, nasarar da jam’iyyar ta samu ba zai rasa nasaba da wannan ziyara ba.

Gwamnan jihar, Willie Obiano ne ya samu mafi yawan kuri’u a Zaben in da ya lashe duka kananan hukumomi jihar 21.

Share.

game da Author