Malaman makarantar Firamare na Kawo dake Kaduna sun kora yara ‘yan makaranta babban titin sabon birnin don nuna fushin su ga sakamakon jarabawar da gwamnatin jihar ta yi wa malaman firamaren jihar inda kashi 75 na malaman jihar ba su ci jarabawar ba.
A makarantar Firamaren, malamai sun kora kananna yara ‘yan shekara 3 zuwa bakwai kan tituna domin taya su yin zanga-zanga.
Iyayen yara sun koka da wannan mataki da malaman makarantar suka dauka. Malam Bala Ali da ya ke zantawa da PREMIUM TIMES HAUSA a Kaduna, ya ce lallai wannan abu da malaman suka yi abin kunya ne kuma ya nuna cewa lallai basu cancanci koyar wa ba.
” Ta yaya za a ce wai malami ya kora yara ‘yan shekara kasa da biyar manyan tituna a gari kan abin da bai shafe su ba. Idan basu ji dadin jarabawar da akayi musu ba sai su fito suyi zanga-zanga ba su tura yaran mutane tituna da ganye a hannun su ba suna ihu. Wannan abu bai kamata ba kuma ina kira ga gwamnati da ta dau mataki akan wannan makaranta domin Allah ne ya kiyaye da wani abin ya faru, sai ace daga Allah.
Iyaye da yawa sun fito tituna suna guje guje wajen neman ‘ya’yan su bayan sunji abinda da malaman makarantar Kawon sukayi.
Bayanai da muka samu ya nuna cewa wasu da yawa cikin yaran sun sami raunuka wajen guje gujen.
Gwamnatin jihar ta sanar da kafa wata kwamit domin duba korafe-korafen malaman da suka fadi domin gyara kuskuren da akayi idan har anyi.