Intels ya roki gwamnatin Najeriya, ya amince da bin tsarin TSA

0

Kamfanin Intels, wanda kamfani ne na hadin guiwa da tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar ya amince zai bi tsarin tara kudade a asusun bai daya na gwamnati, wato TSA, wanda tun a farkon shekarar nan ya ke sa-toka-sa-katsi da gwamnatin tarayya kan batun na TSA.

Wannan amincewa da bin tsarin TSA da Intels ya yi, zai kawo karshen ruguntsimin rikicin da ake yi tsakanin kamfanin da kuma gwanati.

Idan ba a manta ba, Hukumar Shige da Fice ta kasa ta baiwa ma’aikatan Intels ‘yan kasashen waje wa’adin ficewa daga kasar nan ko kuma a fitar da su da karfin mulki nan da ranar 30 Ga Nuwamba, 2017.

Hukumar ta shigi da fice ta bayyana cewa an umarci ma’aikatan na Intels, mallakar Atiku da su fice tun bayan da aka soke yarjejeniyar kwangilar tara kudaden da Intels ke yi wa gwamnatin tarayya a tashoshin jiragen ruwa biyar na kasar nan.

An dai soke yarjejeniyar ne, saboda Intels ya ki amincewa da TSA.

Idan ba a manta ba, Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, a karkashin Hadiza Bala Usman, ta umarci Intels da ta daina tara kudaden da ta ke karba na haraji a bankunan ‘yan kasuwa, ta rika Tarawa a Babban Bankin Tarayya, CBN.

Hukumar ta ce daga cikin asusun CBN ne za a rika baiwa Intels da Gwamnatin kason ribar da kowa ya kamata a ba shi.

Daga nan sai Intels ya ce yawancin kudaden da ya ke gudanar da ayyukan yau da kullum a tashoshin jiragen, duk bankuna ne ke bada rance. Idan aka daina ajiya kuma, to bankunan za su daina bada rancen.

Daga nan ne tirka-tirka ta murde, ta ki ci kuma ta ki cinyewa har yau. Masu lura da al’amuran siyasar Najeriya na lura da cewa rikicin Intels na daga cikin dalilan da Atiku ya fusata ya fice daga Jam’iyyar APC.

Share.

game da Author