Ina nan a APC har abada – Inji Bindow

0

Gwamnan jihar Adamawa Jibirilla Bindow ya ce yananan daram-dam a jam’iyyar APC babu inda zai tafi.

Bindow ya fadi haka ne bayan ganawa ta musamman da yayi da shugaban kasa a Muhammadu Buhari a Aso Rock.

“Ba zan taba fita daga jam’iyyar APC ba domin da ni aka kafa jam’iyyar tare da shugaban majalisar dattijai na yanzu, ka ga ko ai bazan fice daga gidan da aka gina da ni ba.

“ Wazirin Adamawa Atiku Abubakar kamar Uba ne gare ni sannan dattijon arziki kamar yadda wasu dattijan jihar suke kuma haka zan ci gaba da bashi girma kamar kowa.

Da aka tambayeshi kan abin da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai yace wai shine na farko da ya nuna goyon bayan sa ga Buhari, Bindow ya ce, “ ai mu a yankin Arewa maso gabas babu abin da za muce wa Buhari illa Allah ya biya, don irin ayyukan da yayi a yankin musamman wajen yaki da ta’addanci.

“Game da ficewar Atiku daga jam’iyyar APC kuwa, ina ganin Atiku mutum ne da ya mallaki hankali sannan zai iya zartar wa kansa hukunci akan duk abin da a sa a gaba. Yaga haka yafi masa ne.

“APC a jihar Adamawa na nan da karfin ta. Idan ka duba a cikin ‘yan majalisar jihar 25, APC na da 24, sanatoci uku daga jihar duk ‘yan APC ne da kuma da yawa daga cikin yan majalisar wakilai.

Share.

game da Author