Hukumar SON ta kama mota make da Siga a iyakan Kebbi da kasar Benin

0

Shugaban hukumar SON na jihar Kebbi, Jibril Muhammad ya ce sun kama wata babbar mota dankare da buhunan siga.

Ya sanar da haka ranar Litini da yake zantawa da kamfanin dillanci labaran Najeriya a Birinin Kebbi.

Ya ce sun sami labarin shigowa da buhunan ne ta iyakan Kebbi, Benin da jamhuriyyar Nijar daga kasar Brazil.

Muhammad ya ce cikin kwanaki uku da fara aikin hukumar a jihar, sun kama buhunan sigan a cikin kasuwan Birinin Kebbi wanda jimlarsu ya kai 610.

‘Buhunan sigan ‘yan kg 50 da muka kama na dauke da sunan ‘White Crystal Nardini Agro Industrial and LTDA Industrial Brazillaira’ da farashin Naira 15,000 kan kowace buhun a kasuwan Birinin Kebbi wanda jumlar kudin ya kai Naira miliyan 9.15’’.

Share.

game da Author