Hukumar Kwastam ta tallafawa ‘yan gudun hijira da kayan abinci

0

Mataimakin shugaban hukumar kwastam Abdulkadir Azarema ya ce hukumar ta wadata wasu daga cikin sansanonin ‘yan gudun hijira dake jihar Yobe da kayan abinci domin tallafa wa mazauna sansanonin.

Ya ce wannan itace karo na biyar da hukumar ke wadata wadannan sansanoni da urin wadannan agaji.

” Tun daga shekarar 2016 muke raba wa ‘yan gudun hijiran kayan da muka kama a iyakokin kasar nan da ake kokarin shigowa da su.”

” Wannan karon mun bada buhunan shinkafa kg 50 18,968,jarkokin man gyada guda 939, beli 133 na gwanjuna, kwalayen taliya 8,659,katan din tumatir 20, takalma 1,362,maganin sauro 584, jarkan manja 32, atamfa da sauransu.”

Share.

game da Author