Hukumar kwastam dake kula da jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara ta tara Naira miliyan 829.5

0

Hukumar kwastom dake kula da jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara ta ce sun tara Naira miliyan 829.5 daga watan Mayu zuwa Oktoba.

Shugaban hukumar Nasiru Ahmad ya sanar da haka a Sokoto ranar Laraba inda ya kara da cewa sun kama motoci 39 wanda suka kai Naira miliyan 83.6.

Ya kuma ce sun yi kame sau 103 wanda ya hada da kudin duti daya kai Naira miliyan 161.3 tare da motoci 39.

Ahmad ya ce a watan Oktoba sun yi kame sau 23.

“Sauran abubuwan da muka kama sun hada da buhunan shinkafa ‘yan kg 50, 552, jarkunan man gyada 976, belin gwanjuna 209 da kahon giwa biyu wanda ya kai Naira miliyan 14.4.”

“Bara mun tara Naira biliyan 1.1 amma bana mun sami Naira miliyan 829.6.”

Share.

game da Author