Akalla mutane biyar ne aka bada rahoton sun rasa rayukan su a wasu hadurra biyu a titin Lagos zuwa Ibadan da kuma unguwar Kara a cikin Lagos, sakamakon wasu munanan hadurra a safiyar yau Alhamis.
Wanda aka yi hatsarin Kara a gaban sa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa hatsarin ya ritsa da wasu kananan motoci da kuma wata babbar motar daukar kaya. A daidai mayanka, sai wani jirgin kasa ya kauce hanya, inda ya suntuma cikin gungun jama’a, ya ji wa masu jiran mota da dama da kuma ‘yan tireda ciwo.
Shugaban Hukumar Agajin Gaggawa na Jihar Lagos, Adesina Tiamiyu ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da faruwar hadurran.
Shi kuma hadarin da ya afku a kan Gadar Kara, ya haddasa mutuwar mutane biyar kuma wasu 19 sun samu munanan raunuka.
Shi ma kwamandan FRSC na jihar Lagos, Hyginus Omeje, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES faruwar hadarin, inda ya ce mutane uku ne su ka mutu nan take, biyu kuma sai bayan an garzaya da su asibiti.
Discussion about this post