Hukumomi a kasar Misra sun sanar cewa mutane 305 zuwa yanzu aka tabbatar da mutuwan su ba 235 kamar yadda aka sanar a da ba.
Gwamnatin Misra na zargin cewa wannan hari dai ‘yan kungiyar ISIS ne suka kai a wani masallacin juma’a dake tsibirin Sinai daidai suna sallar juma’a.
Wani da yake wurin a lokacin da abin ya faru ya ce maharan sun zo ne a wasu motoci biyar sanye da kayan sojoji, sannan suka bude wuta daidai mutane sun fara Sallar juma’a.
Wadanda ma ba sallah suke yi ba ba su sha ba domin har su an kashe. Sannan ya ce an gansu da tutoci irin na kungiyar ISIS.
Tun daga ranar ne dai gwamnatin kasar Misra ke ta yi wa maboyan ISIS da ke yankin tsibirin Sinai luguden wuta ta jiragen saman ta.