Gwamatin Tarayya ta dauki sabbin masu karbar kudaden haraji daga hannun ‘yan Najeriya har 2,190, yayin da ta tura 1,710 daga cikin su zuwa jihohi daban-daban domin fara aiki.
Wadanda aka dauka din sun hada da masu karbar haraji a yankunan jama’a, masu bibiyar kudin bayyana kadarori da sauran su.
Ministar Harkokin Kudi, Kemi Adeosun ce ta bayayya haka a jiya Lahadi. Ministar ta ce ana tantance adadin yawan harajin da kamfanonin da suka karbi kudaden ayyuka daga Gwamnatin Tarayya suka biya tun daga shekaru biyar zuwa yau.
Adeosun ta yi wannan bayanin ne a Legas a wurin taron hadin guiwa na jami’an Tara Kudaden Haraji da Lauyoyi majibinta hada-hadar haraji a Legas.
Ta bayyana cewa sai dai akasarin jami’an wayar da kan jama’a ne za su yi dangane da biyan haraji.
Kemi ta ce a yanzu haka dai an tura jami’ai 1,710 jihohi 33.
Wadannan jami’ai dai za su rika wayar da kai dangane da fito a biya haraji ko kuma bayyana kadara.
Sai dai kuma daga nan zuwa 31 Ga Maris, to duk wanda bai fito ya bayyana ba, ko bai biya ba, to zai ya karya doka.
Idan ba a manta ba, makonni biyu da suka shige, ministar ta ce gwamnatin Buhari za ta maida hankali wajen karbar haraji, domin kudaden shigar da ake samu daga fetur ba su isa a gudanar da ayyuka.
Ta kuma ce daga cikin ‘yan Najeriya milyan 66 da ya zama wajibi su biya haraji, milyan 16 ne kacal ke biya. A lokacin ne ta ce za a bullo da hanyoyin da kowa zai rika biyan haraji ga gwamnati.