Hanyoyin 9 dake kara kaifin kwakwalwa da rage yawan mantuwa

1

Sau da yawa mutane kan yi fama da yawan mantuwa wanda idan ba a yi takatsantsan ba yakan kawo sabani tsakain aminai ko kuma ‘yan uwa musamman idan abin da ya kamata a tuna din mai mahimmanci ne.

Da akan danganta yawan mantuwa ga tsofaffi ne kawai amma abin yanzu ya zama ruwan dare, ba babba ba yaro.

Sakamakon hakan ne ya sa masana suka yi wani nazari kan haka da gano abubuwan da zai iya sa mutum ya rage yawan yin mantuwa.

A binciken da masannan suka fara yi sun gano cewa shan kayan zaki kamar su alawa, cingam, chakulat da sauran su na taimakawa wajen kara kaifin kwakwalwa.

Da yake wasu ba za su iya mu’amala da wadan nan kayan zaki ba, an zurfafa bincike domin samu wadan su hanyoyi da za a iya bi domin kara kaifin kwakwalwa da rashin mantuwa.

Hanyoyin sun hada da;

1. Samun isasshen barci sannan da yin barci a lokacin da ya kamata.

2. Yin hirar zuci amma ba kowani lokaci ba domin yawan yin hakan na iya sa mutum ya sami matsala a kwakwalwar sa.

3. Yin hira da mutane musamman abokan arziki.

4. Motsa jiki kamar su guje-guje da sauran su.

5. Tsayawa a hasken rana wanda ke bada Sinadarin ‘Vitamin D’ sannan da cikin kayan abincin dake dauke da sinadarin kamar kayan lambu.

6. Yin wasannin da ke sanya tunani kamar chess, Sudoku, lisafi da sauran su.

7. Yin aiyukkan da ba a saba yi ba ko kuma ba a taba yi ba da ziyartan wuraren da ba a taba zuwa ba.

8. Yawan yin dariya wanda hakan ke kawar da damuwa da dodewar kwanya.

9. Cin kayan lambu da ake kira ‘Bule Berries’ domin suna dauke da sinadarorin dake taimakawa wajen hana mantuwa.

Share.

game da Author