Hanyoyi 5 da gwamnati za bi don samun kudaden da za ta yi ayyukan dake kasafin kudin 2018

0

Ministan kasafin kudi da tattalin arzikin kasa Udo Udoma ya zayyano hanyoyin da gwamnati za ta bi wajen samar da kudaden da za ta yi ayyukan da ta sa a kasafin kudin 2018.

Idan ba a manta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudi na naira Tiriliyan 8.6 ga majalisar kasa a makon da ya gabata.

Ga hanyoyin

1 – Na farko za mu kara tsannanta wa wajen karbar haraji sannan zamu kara kudaden shiga ta hanyar karban haraji zuwa kashi 15 bisa 100 daga kasha 6 bisa 100.

2 – Za mu yi amfani da kudaden da muka samu a mai wajen bunkasa fannin da ban a mai ba, daga nan sai muyi amfani da ribar da zamu samu ta hanyoyi biyu Kenan wajen samar da ababen more rayuwa.

3 – Zamu kirkiro wasu hanyoyi da za a dunga samun kudaden shiga a kasar na da za ay amfani da ilimin kimiyya wajen tara kudaden, haraji da bin diddigi sanna kuma zai taima ka wajen gano masu kin biyan haraji.

4 – Gwamnati za ta sake duba yadda kamfanoni ke gudanar da ayyukan su a yankunan da ake hako danyen mai. Za a sake duba shiri da bayanai game da yadda ake sabunta lasisin kamfanonin da tsawon kwanankin da za a yi kafin a sake duba haka.

Bayan haka kuma za a sake komawa teburin shawara da sabunta yanjejeniya da ke tsakanin kamfanonin main a kasahesn waje da Najeriya domin inganta samun kudaden shiga.

5 – Duk da cewa wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati suna kokari wajen samar da kudaden shiga ta hanyar karban haraji, sai sun kara matsawa sosai idan har anaso a cimma burin da aka sa a gaba.

Za a kara seta su domin ganin ba a samu Baraka ba da kuma like duk wata rami da zai iya sa a samu matsala a haka.

Share.

game da Author