Hadin kan Najeriya shi ne mafita, Buhari a Abakaliki

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya kara jaddada muhimmancin hadin kan ‘yan Najeriya a matsayin mafita ga dorewar kasar nan.

Buhari ya yi wannan bayani ne a yau Talata a garin Abakaliki, hedikawatar jihar, Ebonyi, yayin wata ziyarar kwana daya da ya kai a jihar Ebonyi.

Buhari wanda ya kai ziyara a yankin Kudu maso Gabas a karon farko, tun bayan hawan sa mulki, ya ce kasancewar ‘yan Najeriya a matsayin al’ummu daban-daban, wata baiwa ce da Allah ya yi mana ta hada kai domin dorewar zamantakewar mu.

“Zuwa na a nan yau, wani abu ne da ke tabbatar da yakinin da na ke da shi cewa hadin kan Nijeriya shi ne mafita a gare mu. Ba haka kawai muka kasance al’ummu da kabilu masu yare sama da 300 ba.

Buhari ya kuma kara tabbatar wa jama’ar yankin Kudu maso Gabas cewa gwamnatin sa za ta kara gudanar da ayyukan more rayuwa domin a kara gaggauta samar da ci gaban yankin.

Ya ce kasafin 2018 da ya gabatar cikin makon da ya gabata ya na cike da ayyukan ci gaba da za a gudanar a yankin na su.

“Lokacin da na gana da shugabannin yankin Kudu Maso Gabas, cikin watan da ya gabata a Abuja, sun tayar da batutuwa da dama ciki har da matsalar halin da titinan wannan yanki ke ciki. Ina kara tabbatar muku dacewa za mu cika alkawurran da muka yi. Domin kasafin 2018 ya na cike da ayyukan ci gaba da suka hada da titina, lantarki, noma da ababen more rayuwa a wannan yanki.”

Tun da farko Gwamna David Umahi ya nuna farin cikin sa dangane da ziyarar da shugaban kasa ya kai da kuma godiya musamman a kan ayyukan noma da ya bayar da gudummawar aiwatarwa.

Daga cikin manyan da suka tarbi Buhari akwai mataimakin gwamnan Ebonyi, Kelechi Igwe, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, tsoffin ministoci da tsoffin gwamnoni na jihar da sauran manyan baki.

Buhari ya kaddamar da aikin titin da ya tashi daga Abakaliki zuwa Afikpo mai tsawon kilomita 14.5 wanda gwamnatin tarayya ta gina, sai sabbin gadojin sama biyu da aka gina a kan babban titin Afikpo zuwa Enugu.

Share.

game da Author