Ministan wutan lantarki, aiyukka da gidaje Babatunde Fashola ya ce gwamnati za ta kammala gina hanyar Gombe zuwa Biu nan ba da dadewa.
Fashola ya fadi haka ne da ya ke tattauna da manema labarai bayan zaman majalisar zantaswa da akey duk laraba a fadar gwamnati.
Fashola ya ce za a bukaci Naira biliyan 27.233 wajen gina hanyar mai tsawon kilomita 117.
Ya ce gwamnatin jihar Gombe ta gina kilomita 9 na hanyar.
Ya ce gwamnati za ta kammala gina hanyar cikin watanni 24.