Ministan kwadago Chris Ngige ya ce gwamnatin Buhari ta Samar wa ‘yan Najeriya miliyan 7 aikin yi tun bayan darewa karagar mulki.
Ngige ya ce mutanen Najeriya sun Mai da hankali wajen ganin ko mutanen sun Sami aiki a manyan ma’aikatu ne maimakon duba duka bangarori a Kasar nan.
Ngige ya ce fannin Noma kawai ya Samar da aiki Sama da miliyan 5.