Gwamnatin Bauchi ta raba wa cibiyoyin Kiwon lafiya miliyan 46

0

Gwamnatin Bauchi ta raba wa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 16 dake karamar hukumar Dass naira miliyan 46 domin tallafa wa ayyukan su.

Jami’in hukumar NSHIP Adamu Muhammed ya sanar da haka inda ya kara da cewa hukumar ta raba wannan kudade me Kari kan Naira miliyan 28 da ta fara rabawa.

Daga karshe ya ce gwamnati ta zabi wadannan cibiyoyi ne ganin kokarin da suke yi wajen Kula da marasa lafiya a tankin.

Ya ce sun zabi wadannan asibitocin ne bisa ga yanayin kula da mutanen jihar da suke yi

Share.

game da Author