‘Gwamnati ba ta rike kudaden Tallafin Afuwa na daliban masu karatu a kasashen waje ba’

0

Mashawarci na Musamman ga Shugaban Kasa a kan Shirin Afuwa a Yankin Neja Delta, ya bayyana cewa dukkan daliban da ke karatu a kasashen waje a karkashin wannan shiri, an biya kowanen su kudaden karatu, alawus din abinci da na sauran rayuwar yau da kullun da sauran alawu-alawus din da aka saba ba su.

Paul Boroh, wanda tsohon Burgediya Janar ne, shi ne ya bayyana haka a cikin wani bayani da Daraktan Yada Labarai na ofishin Shirin Afuwar, Charles Dafeh ya bayyana a Abuja.

Yayin da ya ke karyata zargin cewa daliban su na bin gwamnatin tarayya bashin kudaden tallafi da sauran hakkokin su, ya ce kashi 90 bisa 100 na daliban za su kammala karatun su ne cikin watan Disamba mai zuwa.

Daga nan sai ko-dinatan ya kara dacewa, idan wadannan kashi 90 suka kammala karatu cikin Disamba, to zai rage sauran dalibai kashi 10 kacal kenan, wadanda za a bari a kasashen wajen a karkashin wannan tsari na tallafin afuwa.

Ya kara da cewa hukuma ko tsarin sa ba shi da wata matsala ko kishkilar biyan dalibai da ke karatu a kasashen waje dukkan hakkokin su.

Share.

game da Author