Gwamna Yari ya yi rangadin sabon ginin Sarkin Gusau da aka kashe wa sama da n iuraira miliyan 500

0

Gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari ya yi rangadin sabon fadar Sarkin Gusau da gwamnati ta bada kwangilar sa akan naira miliyan 505.

Da yake ganawa da wakilan kamfanin da gwamnati ta ba aikin ya yaba ma aikin sannan ya gargadesu da su tabbata sauran aikin da ya rage sun yi shi cikin aminci.

Bayan haka kuma ya duba wasu ayyukan hanyoyi da gwamnati ta bada.

Daga karshe, Yari ya ce ya zauna da rundunar ‘yan sandar jihar da sauran jami’an tsaro domin sanin halin da tsaro take a jihar.

Share.

game da Author