El-Rufai ya na so ya kori malamai ne don ya musanya su da ‘yan kusa da shi – Inji Shehu Sani

0

Sanatan dake wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya ce gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai na so ya kori malaman jihar ne don ya musanya su da na kusa da shi masu yi masa biyayya.

” Koran malamai 21,000 rashin tausayi ne sannan kuma hakan kololowa ce na rashin tunani.

” Yaya za a ce gwamnan da ya kashe naira Biliyan 10 wajen ciyar da yaran makaranta sannan a wayi gari yace wai malaman ma basu kware ba. Gashi wannan abu da ya yi ya sa hankula sun tashi sannan ya kawo rudani a makarantun jihar.

“ Ya yi alkawari cewa zai mai da ‘ya’yan sa makarantun gwamnati idan ya zama gwamna, bai yi hakan ba sai dai ma lalata makarantun da ya yi. Rashin kwarewar malamai ba dalili bane, dama can yana son ya kori malaman da ke da dimbin bashin albashi a kan gwamnatin jihar.

” Duk da cewa da ake yi wai gwamnatin tarayya ta samar da ayyukan yi miliyan 7, sannan kuma gwamnatin jihar na cewa ta kirkiro ayyuka a jihar. An gama shiri tsaf domin yin jana’izan aikin malunta a jihar Kaduna.”

Share.

game da Author