El-Rufai ya ba Fayose ansa kan musanya dakikan Malamai

1

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ya maida wa gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose martani kan zargin da ya yi masa cewa wai yana so ya raba malaman jiha Kaduna da aikin su ne don son rai ba don gyara ba.

“Na sha yi wa mutane gargadin cewa daya daga cikin manufofin jam’iyyar APC shine su kori ma’aikata, kuma gashi sun fara a jihar Kaduna kuma shugaban kasa da kansa ya mara wa gwamnatin jihar baya.”

A martani da ya mai da wa Fayose, El-Rufai ya ce ” Mai girma gwamna ba koran malamai muke yi ba a jihar Kaduna, muna kokarin musanya dakikai ne ciki da wadanda suka kware domin ceto rayuwar ‘ya’yan mu nan gaba.”

Maganar gyara harkar ilimi a Kaduna ya jawo cecekuce sosai inda wasu da yawa suke ganin hakan ba daidai bane, wasu kuma suna ganin abin da gwamnan El-Rufai ke yi abu ne mai kyau domin ceto ‘ya’yan talakawa da kuma samar da ilimi mai nagarta a jihar.

Share.

game da Author