Sanata mai wakiltan Kogi ta Yamma a Majalisar Dattijai, Dino Melaye ya sha ruwan duwatsu a garin Kabba a wajen bukin ranar Kabba da aka yi a karshen makon nan.
Kamar yadda muka Sami labari, abin ya faro ne daidai Dino zai fice daga wurin taron bayan ya kammala bayanin sa.
Yana shiga motar sa sai ko matasa suka fara yi masa ihu suna jifar da.
Gwamnan jihar, Yahaya Bello da ya ke hanyar sa na zuwa wanen taron karewa ya yi ya juya bayan yaji abin da ke faruwa.