Dawo-Dawo gida Atiku – Jam’iyyar PDP na bikon tsohon mataimakin shugaban Kasa

0

Jam’iyyar PDP a jihar Adamawa ta yi kira ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da ya dawo jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar Shehu Tahir, ne ya yi wa Atiku wannan kira a taron jam’iyyar na jiha da akayi a Yola.

Ya ce da ma can bai kamata Atiku ya fice daga jam’iyyar da aka kafa tare da shi ba tun farko.

Ya yi kira ga sauran ‘yan jam’iyyar da su ci gaba da yin kira gareshi da ya dawo jam’iyyar sannan ya ce kofar jam’iyyar a bude take ga kowa da kowa.

Share.

game da Author