Mai ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan harkar tsaro Sambo Dasuki ya bayyana a Kotu yau domin bada shaida kan shari’ar Olisa Metuh.
Hukumar EFCC ne ta maka Metuh a kotu kan wasu kudade da ya waske da su a lokacin yana kakakin jam’iyyar PDP.
Metuh ya bukaci kotu da ta gaiyaci Dasuki domin bada shaida kan kudin da aka ce an bashi daga kudin siyan makamai.