Dan takaran gwamnan jihar Anambra a inuwar jam’iyyar PDP Oseloka Obaze, ya ce sam bai amince da sakamakon zaben gwamnan jihar ba cewa an tafka magudi a zaben.
Ya ce bayan amfani da tsohon rijistan zabe, a wajen irga kuri’u an sami banbancin yawan kuri’u tsakanin abin da naurar ‘Card reader’ ta ba da da wadanda aka irga bayan kada kuri’un.
Ya kara da cewa babu wani bayan haka an sami sabanin yawan kuri’u a wurare da yawa da ya nuna ba a yi gaskiya ba a zaben.
Oseloka Obaze na jam’iyyar PDP ya zo na uku a zaben inda a karo na farko jam’iyyar APC tayi tasiri a zaben jihar in da ta zo na biyu.
Willie Obiano na Jam’iyyar APGA ne ya lashe zaben jihar inda a cinye duka kananan hukumomi 21 na jihar.
Ga sakamakon zaben:
2,064,134 – Wadanda suka yi rijista
Wadanda aka tantance – 457,311
Kuri’un da jam’iyyu suka samu
AA – 66
ADAP – 1,036
ACD – 232
ACPN – 346
ADC – 477
ADP – 603
APC – 98,752
APDA – 2,111
APGA – 234,071
APP – 661
BNPP – 70
DA – 97
DPC – 145
GPN – 41
HDP – 31
ID – 37
KOWA – 49
LP – 963
MMN – 79
MPPP – 39
NCP – 74
NDLP – 33
NEPP – 84
NNPP – 68
NPC – 136
NUP – 69
PDC – 381
PDP – 70,293
PPA – 2,787
PPN – 55
PPP – 87
PRP – 59
SDP – 20
UDP – 222
UPP – 7,903
YDP – 72
YPP- 65
Kari’un da aka yarda da su – 422,314
Kuri’un da ba a yarda dasu ba – 26,457
Kuri’un da aka Kada – 448,771