Tsohon shugaban masu rinjaye a majlisar dattijai Sanata Ali Ndume ya ce bai je kotu don ya tozarta wani bane a majalisa, ya je kotu ne don ya sami fahimtar dalilin da ya sa majalisar ta dakatar dashi.
“ Gaskiya bana so ku dauka wain a je kotu don tozarta wani ne ko kuma wani abu mai kamar haka. Na yi haka ne don in dada gyara demokradiyya a kasar nan. Amma ba don wata manufa ba.
“ Ba naje kotu don son rai na bane, na je kotu ne don in sani ko kora ta da akayi a majalisa daidai ne ko ba daidai ba. Saboda haka abin da nayi ba nayi da wata manufa bace, sannan duk wanda yace nayi ne don son rai, na barshi da Allah.
Ndume ya fadi haka ne bayan zaman a farko da ya halarta a zauren majalisar da yake tattaunawa da manema labarai bayan zaman majalisar na yau.
Yace zai yi tafi kasar saudiyya domin yin Umra, ya gode wa Allah dawowar sa majalisa lafiya.
Discussion about this post