Dalilin da ya sa gwamnati ba ta fara raba wa ’yan kwangila kudin SUKUK ba – Gwamnatin Najeriya

0

Gwamnatin Tarayya ta maida martani dangane da wata ji-ta-jita da ake yadawa cewa tun a cikin watan Satumba aka karkatar da naira biliyan 100 na kudaden SUKUK.

Da ta ke maida raddin, Daraktar kula da ofishin lura da kudaden bashi, Patience Oniha, ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa kudaden na nan ajiye, a Babban Bankin Tarayya a cikin asusun da aka bude na musamman.

Babbar Daraktar ta ce maganar an karkatar da kudin ba ta ma taso ba, domin suna can ajiye. Don haka a ta bakin ta, zargin bashi da tushe balle makama. Kuma tuni aka yi sanarwar gudanar da ayyukan gina titina a fadin tarayyar kasar nan har guda 25 da kudaden na Sukuk.

A ranar 5 Ga Oktober, Ministar Harkokin Kudade, ta mika cakin kudin na SUKUK har naira biliyan 100 ga Ministan Makamashi, Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola a Abuja.

Da ta ke karin bayani a cikin dariya, Oniha ta ce, “Ai kudin Sukuk ba su ma iya shiga cikin asusun kudaden da gwamnatin tarayya ke gudanar da wasu ayyuka da su,”

Ta kara yin karin hasken cewa su fa kudaden Sukuk su na da tsari na su yadda ake rarraba su ga masu kwangiloli, shi ya sa kafin a raba su sai dan kwangila ya kawo wasu takardun cancanta tukunna, kafin a amsa.

“A matsayin da muke wajen raba kudaden SUKUK, shi ne mun umarci kowane dan kwangila da ya gabatar mana da takardun bayanan kamfanin sa ta yadda za mu gamsu da ingancin kamfanin na sa kafin mu fara raba musu kudaden.”

Share.

game da Author