“Da alawar naira 10 nake rudar ‘yar shekara 9 na kwanta da Ita”- Inji Abubakar

0

Ana tuhumar wani matashi mai suna Mohammed Abubakar, dan shekara 30 a hukumar kare hakkin yara kanana na jihar Neja saboda kama shi da laifin aikata lalata da wata yarinya ‘yar aji hudun makarantar firamare ‘yar shekara 9.

Da yake amsa laifin sa Abubakar mazaunin unguwan Tudun Fulani, karamar hukumar Bosso, ya ce yakan bata alawa ne irin ta tsinken nan na naira 10 sannan ya kai ta wani kangon gina da ba a gama ginawa ba ya yi lalata da ita.

Ya ce dalilin aikata hakan kuwa shine don matar sa na jego kuma gashi sha’awa na yawan kama shi. Da ya taya yarinyar da alawa yaga babu matsala sai ya ci gaba da buga harkar sa kullum ya zo kusa da makarantar yaran.

Ya roki hukuma ta yafe masa.

Itako yarinyar ta ce tunda ya bata wannan alawa kullum sai ta fito lokacin tara, daga nan sai su tafi wannan gini su yi abin da suke yi kullum.

Malaman makarantar da ta kama su ta ce, ta fara gane wani abu na faruwa ne tun da ta ga yarinyar ba ta dawo wa aji bayan hutun tara.

“ Daga nan ne na fara sa mata ido inda wata rana da ta dawo aji gab da za a tashi mu ka kai ta ban daki muka duba gabanta sai muka ga lallai akwai abinda ke faruwa da ita. Ana haka ne fa washe gari lokacin tara muka bi ta a boye muka kama su kuwa a daidai suna aikata wannan fitsara.”

Yanzu dai ita yarinyar na asibiti ana duba ta sannan shi kuma Abubakar an mika shi ga hukuma.

Share.

game da Author