CIYAR DA DALIBAI A JIGAWA: Gwamnati zata kashe naira Miliyan 147 duk mako

0

Gwamnatin tarayya ta fara ciyar da daliban firamare dake makarantun gwamnati a jihar ‘yan aji 1 – 3.

An kadamar da wannan shiri ne ranar Laraba a makarantan firamaren ‘Nuhu Muhammad Sunusi’ dake Dutse.

Da yake tofa albarkacin bakin sa mataimakin gwamnan jihar Hassan Ibrahim ya ce shirin za ta ciyar da yaran firamare 726,033 a jihar.

Ya ce za a kashe Naira miliyan 147 duk mako wajen ciyar da yaran sannan sun dauki masu girki 30,000 domin hakan.

” Taimakon da wannan shirin ta yi bai tsaya ga bunkasa ilimi a jihar da samar da aikin yi wa mutane ba domin ‘yan kasuwa kamar mahauta, masu siyar da hatsi da kayan abinci suma za su amfana da wannan shirin.”

Ya kuma kara da cewa nan gaba jihar za ta fara ciyar da sauran daliban dake aji 4 zuwa 6.

Share.

game da Author