CANJIN SHEKA: Me ke laifin Atiku Abubakar?

0

Ba kan sa farau ba, kuma daga Atiku Abubakar za a daina canjin shekar siyasa a Nijeriya ba. Yawancin wadanda suka ci moriyar zaben 2015, duk albarkacin canjin sheka ne, sai kuma gamin-gambizar da aka rada wa suna APC har jam’iyyar ta yi gamo da katarin karbe mulki a hannun PDP.

Matsalar Atiku Abubakar ta faru ne tun daga lokacin da aka ba shi takarar mataimakin shugaban kasa a karkashin PDP a zaben 1999, bayan ya rigaya ya ci zaben gwamna a Jihar Adamawa.

An fara yin kaffa-kaffa da shi saboda take-taken sa da shugaban kasa na lokacin, Olusegun Obasanjo na kallon Atiku na kokarin neman takarar shugabancin kasar nan.

A yadda aka san dan siyasa, tun daga kan kansila har kowa ma, babban burin kowa shi ne ya matsa a mataki na gaba. Shin Atiku ya yi laifi don ya fara kanne ido ya na leken kujerar shugaban kasa wadda ke a cikin fadar da ya ci kowa kusanci da fadar. Shin daga mataimakin shugaban kasa, me dan siyasa zai neman? Ciyaman na karamar hukuma ko kuwa dan majalisar tarayya.

Yanayin yadda ake tafiyar da siyasar Nujeriya lalatacce ne, gurbatacce kuma karkatacce ne. Gwamnonin kasar nan sun taimaka wajen dagula siyasar kasar nan, kuma kowa ya zuba musu ido.

Bukatar kowane mataimaki shi ne ya zama gwamna. Na shugaban kasa kuma ya zama shugaba shi ma. Amma kiri-kiri gwamna bai yarda mataimakin sa ya gaje shi ba. Kamar yadda shi ma shugaban kasa bai yarda mataimakin sa ya gaje shi ba. Alhali kuwa duk wanda ka ga an ba mataimaki, to ana ganin idan ba a ba shi ba, to kuwa ba za a yi nasarar zabe a dukkan kanana hukumomin shiyyar da ya fito ba.

Shi kuwa gwamna babban burin sa idan ya kammala zabe, to ya zama sanata, ya tafi Abuja ya yi likimon sa a can, ya na cin abin da ya tara a shekaru 8 da ya yi ya na mulki, sannan kuma ya na fin talakawa cin kason da gwamnatin tarayya ke rabawa a Abuja.

Atiku Abubakar dai da shi aka yi fafutikar neman dawo da dimokradiyya daga hannun sojoji. Kuma tare da shi aka kafa PDP wadda ta yi mulki a 1999 zuwa 2015.

Idan aka duba tarihin cin amana, butulci, wulakanci da tozarci a siyasar Nijeriya, bayan PPD ta kafa mulki, Atiku ne aka fara yi duk wani launin rashin mutunci – mai kala ko fari da baki.

Bayan sun sha wahalar kafa jam’iyya, bayan kuma an sasanta da Shugaba Abdulsalami Abubakar, aka je har kurkukun Gashua aka fito da Obasanjo.

A lokacin Obansanjo ya yanke kaunar sake zama wata tsiya a Nijeriya. Ba zan manta ba, daga cikin wanda suka je fito da Obasanjo ya taba shaida min cewa da aka fito shi ke rike da babbar-rigar Obasanjo.

Sai da aka yi tafiya mai nisa Obasanjo ya ce ya manto wata tsohuwar fankar sa a kurkuku. Kuma sai da aka koma aka dauko masa abin sa.

Ba Atiku ne kadai ya fice daga jam’iyya ba don bai samu takara ko don neman takara ba. Buhari ya fice daga ANPP suka kafa CPC, bayan ya yi takara say biyu bai ci ba.

Bayan an kayar da shi a zaben 2911, a karo na uku kenan, ya fito ya shaida wa duniya cewa ya hakura ya daina takara. Har kukan takaici sai da ya yi a gaban bainar jama’a.

A 2011 Atiku ya taka muhimmiyar rawa a wajen bai wa Muhammadu Buhari gudummawa, duk kuwa da cewa ya na PDP ne a lokacin.

Kwakkwarar majiya ta tabbatar da bayan Goodluck Jonathan ya kada Atiku a zaben-fidda-gwanin PDP na 2011, kafin zabe sai da Atiku ya aika wa Buhari gudummawa ta daruruwan milyoyin nairorin da kusan a Nijeriya babu wanda ya bada kamar tasa.

Atiku ne ya na hankalin gwamnonin PDP kuma ya rinjaye su suka fice daga taron PDP, a cikin Dandalin Eagle Square, a Abuja, inda suka taru a Cibiyar Taron ta Shehu ‘Yar’Adua. Wannan ne sanadiyyar karya PDP.

Kafin Atiku ya fice daga PDP, ya bayyana irin zaman agolancin da wasun su ke yi a jam’iyyar, alhali kuwa su ne ‘ya’yan fari. Ya fadi irin mulkin-mulaka’u da karfa-karfa da ake yi, da kuma kwatagwalcin da gwamnatin Jonathan ta rika yi a da sunan mulki.

Bayan ya bayar da dimbin gudummawa duk da cewa Buhari ya kayar da shi a zaben-fidda-gwani, Atiku har sadaukar da Garba Shehu ya yi ga Buhari. Garban nan dai da kowa ya sani a matsayin babban gogarman kare Atiku, a lokacin da aka yi ta tabka balahira da Obasanjo, kafin saukar gwamnatin sa.

Bayan APC ta kafa mulki, akwai manyan ‘yan asalin PDP wadanda a yanzu haka su ke jikin gwamnatin Buhari, kuma akwai tuhumar kotu a kan kowanen su ta bilyoyin nairori. Amma a zaman yanzu su ke fada-a-ji.

Har yau babu wata tuhuma a kan Atiku, ko shaida bai taba zuwa kotu ba. Sai ma karar da ya taba kai Obasanjo, har ya kayar da shi sau biyar kafin saukar su kan mulki.

Gwamnatin APC ta kamo hanya gadan-gadan ta karya Atiku. Kamfanin sa INTELS da ya kafa a lokacin da ko ofis ba su da sukunin budewa, sai dai suka bude a cikin kwantina, ya yi karfin da a yau a harkar fiton manyan jiragen ruwa masu dakon danyen mai babu kamar sa. Kuma shi ne mafi shahara wajen tara wa Nijeriya kudin haraji a tashoshin jiragen ruwan kasar nan.

A shekarun da Atiku ya yi ya na fada da gwamnatin Obasanjo, ko mummunar harara bai yi wa INTELS ba, balle ya nemi karya shi. Haka marigayi Umaru, wanda PDP ta wofintar da Atiku ta dauke shi, shi ma bai nemi karya Atiku ba.

Duk da irin yadda Atiku ya shige gaba aka karya PDP a zamanin Jonathan, shi ma Jonathan bai nemi karya kamfanin Atiku ba. Sai gwamnatin Buhari, gwamnatin yaki da cin hanci da rashawa.

Akwai sama da manyan ‘yan siyasa 20 a cikin gwamnatin Buhari, wadanda ba wanda kotu ba ta daure a kurkukun Kuje ba, saboda zargin rub-da-ciki da bilyoyin nairori. Da yawan su ma yanzu sanatoci ne, kuma shari’ar su nema ta ke ta susuce. Har yau ba a yanke wa ko daya tilo hukunci ba. Shin da Atuku ake so a yi zakaran-gwajin-dafi kenan?

Da yawa masu kallon cewa ana yi wa Atiku bi-ta-da-kulli ne, su na nuna cewa a lokacin da gwamnatin Buhari ke gallaza wa Atiku, a daya gefen kuma an rufe ido wajen ganin wani aibi ga Bola Tinubu, shi ma daya hamshaki na yanzu wanda ya yi gwamna shekara takwas a Lagos.

Ana ganin cewa Bola Tinubu ne ma ya fi kowa cin moriyar gwamnatin Buhari, idan aka yi la’akari da mukaman da aka bai wa yaran gidan siyasar sa ‘yan yankin Kudu-maso-Yamma.

Siyasa dai an ce romon jaba ce, ga kitse kuma ga wari. Mai yiwuwa Atiku ya yi babban kuskure fitar da ya yi daga APC. Zai iya yiwuwa kuma shi ma ya tsinci same a jarabawar neman taraka karo na hudu da zai yi nan gaba. Musamman idan wash hasalallu daga APC suka fice suka bi shi.

Idan ma bai yi nasarar ba, to su dai magoya bayan sa na ganin ficewar sa it’s ce alheri.

Share.

game da Author