CAN ga OSINBAJO – “Kai dai baka sani bane amma ana shiri a boye don a mai da Najeriya Kasar Musulunci”

0

Kungiyar kiristocin Najeriya CAN ta mayar wa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo martani kan cewa da yayi amincewa da shirin lamini na Sukuk abune mai kyau kuma ba anyi don a mai da kasa Najeriya kasar musulunci bane.

Idan ba manta ba Yemi Osinbanjo a taron Fastoci da aka yi a jihar Legas ranar Juma’a ya kwabi korafin da kungiyar CAN ta yi na cewa gwamnatin kasar nan na kokarin mai da Najeriya kasar musulunci da kirkiro da shirin lamuni na Sukuk da tayi.

Ya ce tabas shirin Sukuk shiri ne na musulunci amma duk da haka kasashen da ba ma na musulunci ba sun fi morar shirin da ya hada da kasahen Amurka,Sin, Afrika ta Kudu da sauran su.

” Ba ta yadda aka sami kudin ya kamata ace ya dame mu ba. Yadda aka kashe su ne ya kamata ace ya fi damun mu.”

Duk da wannan bayanan da Osinbajo yayi, kungiyar CAN ta ce mataimakin shugaban kasa bashi da cikakken masaniyya kan shirin gwamnati na boye na yin amfani da irin wadannan shiri dom mai da Najeriya Kasar Musulunci.

Bisa ga bayanan da shugaban kungiyar Sanson Ayokule ya yi wanda darektan yadda labarai na kungiyar Adebayi Oladeji ya karanta yace bincike ya nuna cewa a shekaran 1983 kasashen da ke cikin kungiyar ‘Organisation of Islamic Countries’ sun hadu a kasar Landan in da aka kirkiro wasu shiri na boye domin mai da wasu kasashen Afrika kashen musulunci ciki har da Najeriya.

Ya ce wannan ba boyayyar abu bane domin za a iya samun cikakken bayanin a yanar gizo.

Kungiyar ta ce ba adawa ta ke yi da addinin musulunci ba, abin da yake ci mata tuwo a kwarya shine kirkiro shirye -shirye da ake yi a kasar nan yanzu wanda kiri-kiri shiri ne na neman mai da kasar nan kasar Musulunci.

” Abin damuwa ne yadda Najeriya ke hada kawance da amincewa kudurorin kungiyoyin musulunci daga kasashen waje wanda hakan ya karya dokar kasan amma mataimakin shugaban kasa ya kasa gane haka musamman wannan zancen Sukuk. Abin tambaya a nan shine shin doka ta amince da Sukuk din nan ne ko A’a, sannan kuma shi sukuk din nan dai duk ta inda ka biyo abune na musulunci domin cusa shi ga kasashe don musuluntar da su.

Wani babban Lauya, Jiti Ogunye ya wannan korafe-Korafe da CAN take ta yi kan wannan shiri na Sukuk bai taso ba saboda tabbas babu abin da ya hada shi da mai da kasa kasar musulunci. Ya ce kada a ga laifin kungiyar CAN saboda kiyayya da suka nuna na wadannan shirye-Shirye, yace ” Kada a ga laifin rashin fahimtar kungiyar CAN duk da bayanan da mataimakin shugaban kasa yayi domin hakan na da nasaba da wasu munanan kudurori da gwamnatocin baya suka dauka wanda hakan zai sa a dunga yin taka tsan-tsan da abin da gwamnati ke yi ko kokarin yi.”

‘‘Bayanin shine Najeriya na kokarin karban bashi daga wajen bankin da ta sani ne domin ita menba ne a banki sannan ita CAN ba tana cewa kada Najeriya ta zama menban bankin bane amma kada ta karbi bashi daga wannan bankin wanda hakan bai dace ba’’.

Daga karshe Ogunye ya yi kira ga kungiyar CAN da ta nisanta kanta daga yin irin wadannan korafe-korafen marasa amfani domin hakan zai iya zubar mata da mutunci da daraja da take da shi a idanuwar mutanen kasar na.”

Share.

game da Author