Buhari za muyi a 2019 – Jam’iyyar APC, reshen jihar Filato

0

Jam’iyyar APC reshen jihar Filato, ta yi wa Shugaba Muhammadu Buhari mubayi’ar amincewa a matsayin dan takarar ta na zaben shugaban kasa a 2019.

Shugaban jam’iyyar ne na reshen jihar, Latep Dabang, ya bayyana masu ruwa da tsakin jam’iyyar sun amince a bai wa Buhari takarar 2019.

““Mambobin mu na majalisar tarayya da na majalisar jiha da sauran masu ruwa da tsakin jam’iyya duka, a yau Alhamis mun zartas da amindwar mu cewa Shugaba Muhammadu Buhari ne dan takarar shugaban kasar mu a zaben 2019.”

Da ya ke magana kan kalubalen da jam’iyyar ke fuskanta wajen shirye-shiryen zaben kananan hukumomi da ke tafe, shugaban jam’iyyr ya ce jam’iyyar APC ta karbi korafe-korafe har 74 daga cikin zaben fidda-gwanin na kansiloli 325 da aka gudanar.

Ya kara da cewa jam’iyyar ta kafa kwamiti da zai yi nazarin kowane korafi tare da gano yadda za a magance su.

Sai dai kuma ya ce wadannan korafe-korafe ba alamu ne da ke nuna cewa akwai baraka a cikin jam’iyyar ba.

Tun da farko sai da Mataimakin Kakakin Majalisar jihar, Saleh Shehu, ya yi taro manema labarai a ranar Laraba, inda ya sha alwashin kin amincewa da sake yin zaben raba-gardama a Karamar Hukumar Kanam ta cikin jihar Filato.

Share.

game da Author