Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jajanta wa jam’iyyar sa ta APC saboda rasa daya daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar a makon da ya gabata.
Buhari ya fadi haka ne cikin barkwanci da yake gaisawa da shugaban jam’iyyar APC John Oyegun a fadar shugaban kasa wajen rantsar da mambobin kwamitin sake dubawa da tsara fasalin karancin albashin ma’aikatan gwamnati.
Shigowar Buhari ke da wuya sai ya fara yi wa sauran wadanda suke zauran barkwanci.
Gwamnan babban bankin Najeriya da gwamnan Osun Aregbesola ba su tsira da ga ba’ar Buhari ba.
” Duk da cewa babu sunan gwamnan babban bankin Najeriya jawabi na, ban isa ba dole ne in ambaci sunan sa a wannan zaman.” Buhari ya ce.
Shima Aregbesola da yake dana shi, ce masa yayi ya kamata ya dinga saka kaya Kamar yadda gwamnan Kebbi ya sa. Ya duba jikin sa ne ya ga babu bajen tunawa da mazan jiya. Nan dai a aka dara kafin aka dauki hoto.