Buhari ya aika da sakon taya murna ga Obiano

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika da sakon taya murna ga zababben gwamnan jihar Anambra Willie Obiano.

Willie Obiano ya doke abokanan takaran sa 36 a Zaben gwamnan jihar da aka yi a karshen makon da ya gabata.

Buhari ya ce ya yi matukar farin ciki kan yadda a ka gudanar da Zaben cikin kwanciyar hankali ba tare da an samu wani tashin hankalin da ya gagari jami’an tsaro ba.

Ya yi Kira ga gwamna Obiano da ya ci gaba da ayyukan ci gaba da yake yi wa mutanen jihar na samar musu da ababen more rayuwa da sauran su.

Daga karshen ya yabi kokarin da hukumar zabe tayi da Kira gareta da ta gyara inda aka samu matsaloli domin ta gyara.

Share.

game da Author