Akalla mutane biyar aka bada rahoton Boko Haram sun kashe, tare da kona gidaje a kauyen Wuna, cikin Karamar Hukumar Madagali, jihar Adamawa.
Wannan hari ya zo ne kwanaki kadan bayan wani hari da Boko Haram din ta kai a wani masallaci yayin da ake sallar asubahi, inda aka kashe sama da mutne 5O a Mubi, Adamawa.
Majiya ta ce maharan sun yi wa kauyen wanda ke kusa da garin Gulak rubdugu da bindigogi inda suka bude musu wuta.
“Sun shigo kauyen su na harbe-harbe, hakan ya sa aka firgita kowa ya gudu. Sun kashe mutane, suka kona gidaje da hatsi, sannan suka arce da dabbobi” Inji majiyar.
Sai dai kuma wata majiya ta ce sun kai harin ne domin su saci abinci da kuma magunguna.
Shugaban Karamar Hukumar Madagali, Yusuf Muhammadu ya tabbatar da kai harin a ranar Laraba da dare.
Discussion about this post