Bayan kwanaki 81 da dawowa daga jinya, har yau Buhari ya kaurace wa ofishin sa

0

Kwararan majiya daban-daban sun tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa yau kwanaki 81 kenan tun bayan dawowar Shugaba Buhari daga hutun jinya a Landan, amma har yau bai shiga ofishin sa da ke cikin Fadar Shugaban Kasa ba.

Buhari ya bar Najeriya zuwa jiyya a karo na biyu ranar 7 Ga Mayu, ya dawo ranar 19 Ga Augusta, ranar wata Asabar.

Ranar Litinin 21 Ga Agusta, sai bai shiga ofishin sa ba. Ya yi zaman sa a wani karamin ofis da ke a jikin gidan kwanan sa a Fadar ya rika gudanar da ayyuka a ranar.

Ganin cewa a ranar bai shiga ofis ba, sai ‘yan Najeriya da dama suka rika yayata shakkun da ke zukatan su, su na cewa watakila fa Buhari bai gama warwarewa ba ya dawo Najeriya, saboda kawai masu zanga-zangar ya dawo ko ya sauka sun matsa masa lamba a nan gida Najeriya da kuma can birnin Landan.

To daga nan ne sai Fadar Shugaban Kasa ta fitar da wata sanarwa cewa Buhari ya kaurace wa ofishin sa ne, saboda gyare-gyare da ake kan yi a ciki.

Femi Adesina ya ce: “Ofishin Shugaban Kasa ya na bukatar gyara ne, saboda ya yi kwanaki 103 ba ya ciki. Dalilin haka akwai wasu wurare da suka lalace, suke bukatar gyara.”

Bayan wannan sanarwa, sai Garba Shehu ya yi bayani daga baya, inda ya nuna cewa beraye ne su ka yi wa wasu sassa na ofishin illa, saboda ya kasance a kulle tun bayan tafiyar Shugaban Kasa jiyya.

HAR YAU BAI SHIGA OFIS DIN BA

Sai dai kuma kididdiga ta nuna cewa yau kwanaki 81 kenan da dawowar Buhari daga jiyya, amma har yau bai ma leka ofishin ba.

Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa da kuma masu zuwa kai ziyara sun tabbatar da cewa har yau Buhari a karamin ofishin sa ya ke zama,ya yi aiki, ba babban ofishin Shugaban Kasa ba.

Akwai kuma wani ofishin da ya ke amfani da shi baya ga na jikin gidan sa. Shi ne wanda ke jikin Babban Dakin Taron Fadar Shugaban Kasa.

A ranar 30 Ga Oktoba, Buhari ya karbi bakuncin Bila Tinubu, uban jam’iyyar APC a wannan ofishi da ke jikin Babban Dakin Taro.

ANA DANGANTA BATUN DA ASIRI

Ana rade-radin cewa kaurace wa ofis da Buhari ya yi na da nasaba da kalubalen da ya ke ta fuskanta ne na rashin lafiyar da ta tasa shi a gaba har ya kasa zama kasar nan a baya.

‘Yan gaje-gani na cewa wasu malamai ne da suka yi wa Shugaban Kasa aiki, su ka ba shi shawarar da ya kaurace wa amfani da ofishin.

“A gaskiyar magana fa sammu aka yi wa mutumin. Duk wata magana game da rashin lafiyar da ke damun sa fa duk ji-ta-ji-ta ce kawai. Ba wanda zai iya ce maka ga abin da ke damun sa. Hatta kan su likitocin.” Haka wani hadimin Buhari ya shaida wa PREMIUM TIMES, kuma ya roki mu boye sunan sa.

“Ba zato, ba shiri aka garzaya da shi Landan a cikin watan Mayu. Duk wani bincike an yi har a kasar Jamus, amma ba a gano komai ba. Ai dalili kenan muka dukufa addu’o’i kawai.” Inji majiyar PREMIUM TIMES.

AIKIN KARYA SAMMU

Majiyar ta ci gaba da cewa: “Yanzu haka ana nan ana aikin warware sammu ko asiri a ofishin da kuma sauran wasu sassa na Fadar Shugaban Kasa, domin kada asirin ya sake tasiri a kan sa nan gaba.”

FADAR SHUGABAN KASA TA YI MAGANA

Yayin da aka tuntubi Fadar Shugaban Kasa, sai Garba Shehu ya ce Shugaban Kasa ai ya na da ikon da zai iya aiki ko ma daga ina ne a cikin Fadar sa, tunda ba ofishi daya ya ke da shi ba.

Da aka tambaye shi iyar ina aikin gyaran barnar da ya ce berayi sun yi ta tsaya, Shehu bai ce komai a kai ba.

Yayin da Shugaban Kasa na da ikon ya gudanar da sha’anin mulkin sa daga kowane ofis a Fadar Shugaban Kasa, kamar yadda kakakin sa Garba Shehu ya bayyana, ‘yan Najeriya za su ci gaba da waswasin shin sai yaushe Shugaban Kasar zai koma katafaren ofishin nasa.

Share.

game da Author