Akalla mutum 50 ne suka cimma ajalin su a wani hari da wadan su da ake zaton barayin Shanu ne suka Kai wasu kauyukan Shinkafi, jihar Zamfara.
Wani mazaunin garin Shinkafi da ya zanta da PREMIUM TIMES HAUSA ya ce ” Idan ance mutane 50 ne suka mutu an dai fadi ne kawai amma tabbas yafi haka. Wannan matsala na hare-hare ya zama ruwan dare a kauyukan Zamfara. Domin da yawa sun shigo garin Shinkafi ne neman mafaka.
“Kauyukan sun hada da Tunga Kabau, Faro, Mallabawa da Kubi. Bayan kashe mutane da suka yi sai su banka wa kauyen wuya. Wasu da yawa sun gudu wasunsu sun shigo Shinkafi, gudun na tsira.”
Mutanen wadannan kauyuka sun rasa rayukan ‘yan uwan su da dukiyoyin su.
Wasu mazauna Zamfara sun koka da yadda gwamnan jihar AbdulAziz Yari ya ke gudanar na Mulki a jihar, cewa gwamnan baya tare da mutanen sa.
” Idan Ka duba gwamnan Zamfara, Yari, mutum ne da ba ya zama da mutunen jihar ballantana ya kai ga ziyaran kauyuka a jihar. Kullum ya na Abuja mutanen sa kuma na fama da bala’i. Muna rokon sa ya dan dawo Zamfara ko da na wata daya ne cur ya zauna da mutanen sa.” Inji wani mazaunin garin Shinkafi.