Bankin Duniya ta amince ta ba El-Rufai bashin Dala miliyan $350

0

Sanin mai karatu ne cewa gwamnatin jihar Kaduna tana neman karbar bashin kudi na dala miliyan 350 daga bankin duniya domin kammala wasu ayyukan ci gaba da ta faro da Kuma sabbi da zata yi a jihar.

Wannan bashi da gwamna El-Rufai ya ke nema ya sa ana ta tada jijiyoyin wuya inda wasu ke ganin jihar bata bukatan karbo bashi domin gudanar da ayyuka a jihar.

Sanata Shehu Sani shine shugaban Kwamitin majalisa da zata amince da karbar wannan bashi kafin majalisa ta amince ta sa hannu a takardar karbo bashin.

Abin dai ya na neman ya zama da kamar wuya ganin cewa gwamna El-Rufai ba sa ga maciji da Sanata Shehu Sani.

Kwamishinan kudin jihar Kaduna, Abdul Maikwari a hirar da yayi da gidan talabijin na Channels ya ce bankin duniya ta amince ta ba jihar Kaduna bashin sai dai har yanzu suna jiran majalisar Dattijai ne ta sa hannu kafin bankin duniya ta saka ma Kaduna kudin.

Ya ce da zaran hakan ya samu gwamnati zata mai da hankali wajen ci gaba da samar wa mutanen jihar ababen mure rayuwa ta hanyar inganta kiwon lafiya, makarantun da sauransu.

Share.

game da Author