Jami’in kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO Bezu Beshir ya ce tsakanin watannin Janairu zuwa Oktoba na wannan shekara yara 507 ne suka kamu da cutar bakon dauro a kananan hukumomi 20 dake jihar Bauchi.
Ya ce sun sami tabbacin yawan adadin yaran da suka kamu da cutar ne bayan sun gwada jinin yara 162 inda 56 daka cikin su ke dauke da cutar.
Sakamakon haka wani jami’in wayar da kan mutane kan al’amuran kiwon lafiya na jihar Ribado Jibrin yace za su fara gudanar da allurar rigakafin cutar Bakon dauro a kananan hukumomin dake jihar.
Ya ce a wannan karon jihar za ta yi wa yara miliyan 1.7 masu watanin 59 zuwa shekaru 9 alluran rigakafin cutar.
Ya ce za su fara gudanar da kashi na farko daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa 5 ga watan Disamba a kananan hukumomin Alkaleri, Bauchi, Bogoro, Darazo, Dass, Giade, Jamaáre, Kirfi, Tafawa Balewa, Toro da Warji.
Ya ce za su sanar da ranar da za su gudanar da alluran rigakafin kananan hukumomin dake kashi na biyu bayan sun kammala na farkon.
Kananan hukumomin da ke karkashin kashi na biyu sun hada da Dambam, Gamawa, Ganjuwa, Itas Gadau, Katagum, Misau da Ningi.
Discussion about this post